Dyowa whatsapp 76 Instagram 2022

 Assalamu alekun yan owa barka dazuwa shafin tanimu1 tv channel 


Yauma kamar kullin munkawomaku wani saban whatsapp Instagram 2022

Maban mamaki


       👇👇

DOWNLOAD DYOWA 76

           👇👇👇

 

DOWNLOAD THEMS
 

        👇👇

SUBSCRIBE MY CHANNEL
 


TAMBAYA

=========


Assalamu alaikum warahmatullah, da ftr malm yawuni cikin koshin lfy, malm don Allah munaso ayi mana Jan hankali dan nasihohi akan aure da kuma da kuma abinda sunnah tazo dashi akan auren da aka kulla ba tareda an tsawwalama ango ba, ko kuma an tsauwalama gidan amarya, Allah ya sakama malm da gidan aljannah ameen s ameen.



AMSA

=====


Shi Aure Ibada ne. Kamar yadda Wasu Suke kallon Auren a Matsayin Ibada Mai Zaman Kanta. Domin ta Hanyar Aure ne Ake Samar da Mutum. Wanda Kuma duk Wanda Aka Same Shi ko Aka Sameta ta Hanyar Soyayya ga Wani Mutum da ban ko ta raping ko Kuma ta Wata dabara da shi Wannan Namijin ya yiwa Wannan Matar, Domin Akwai Matan da Ake Iskanci da su ta Hanyar dabarar Za'a Aure Su Ayi Fasikanci dasu Kuma su Sami Ciki Harma su Haihu. Sabida Wasu Mazan suna yiwa Mata dabarar zasu Auresu, sabida sunga Auren Suke So, Sai su yaudaresu su kaisu wani Wuri suyi Lalata da su Kuma su dauki Ciki, harma Su Haihu. Wannan ya faru babu Adadi, Kinga kenan Irin Wadancan Mutanen Ba Zaki hada su da wadanda Suka zo Neman Auren diyarku ba. Duk Wanda ya zo Neman Auren diyar ku. Mutunci ne ya Kawo Shi. Tinda Kuwa Haka ne. Inaga Bai Kamata Ku Tsawwala Masa ba. Wajibi ne ku Tausaya Masa Kuma ku Saukaka Masa.

 Wasu Mutanen Kuwa, suna Kallon Aure ne a Matsayin Al'ada. Musamman ma a kasar Hausa. Ita Kuma Al'ada Wani Lokacin Rusa Ibada take Yi. Ko Kuma ta Hana Wasu ma yin Wannan Ibadar yadda ya kamata.

  Al'adun Aure Sun Hana Wasu Mazan yin Aure, Alhalin Kuma Suna so suyi Wannan Auren, Ba Wai Don ba sa So ba. Sai don Sabida Tsawwalawa a harkar Wannan Auren. Duk da cewar babu lefi Mutane su Sanya Al'adar da ta dace da yankinsu a Cikin Auratayyar su, matukar dai ba su Tsawwalawa Al'ummarsu ba.

  Za'a Duba aga Wacce Irin Dukiya za'a Karba a hannun duk Wanda yake da niyyar yin Aure a Wannan Yankin, ta yadda kowa zai iya Yi. Kar a Sanya Wata Al'ada Wadda Zata Hana Wasu yin Wannan Auren. Domin wadanda Ba zasu iya yin Wannan Auren ba. Za'a wayi gari tunanin su Yana chanjawa sai a wayi gari suna Lalata Muku diyanku. Suna tafiya Suna Barinsu. Wanda Kuma Yake da Hali. Zai iya yiwa Matarsa duk Abinda ya gadama idan ta je gidansa. Tinda Matarsa ce. Sabida Akasari Ita Al'ada Bata banbace Mai Wadata da Kuma Talaka. Wanda Kuma Abin ba zai zo daidai ba Gaskiya.

 Idan Wani ya yiwa Matarsa Abu kaza. Wata ma idan anzo Neman Aurenta Zata ce sai anyi Mata Irin wannan abinda aka yiwa wance. Alhalin Kuma Samunsu ba daya bane.

 Tsawwalawa a Harkar Aure ne ta sa wasu mazan Suke Zina da 'yayan Mutane. Wanda da ace ana Sassautawa Kowa zai Auri Matar da yake so daidai karfinsa. Sai kuga Dan da nan yayanku suna Samun mazajen Aure. Amma Wannan rashin Samun Mijin Auren. Yana da Alaka da Tsawwalawa da Wasu Yankin Suke yi ta Fuskar Auratayya. Idan Kuma bayan an Saukaka  Al'amarin Aure, sai aka samu Wani ya lalata mace. Sai a dauki mataki Mai tsauri akansa. Domin Wannan Shaidani ne da yake son Sai ya Gurbata Al'ummarsa.

  Da Wannan ne zaka ji ana cewa a Jiha Kaza. Iyayen Mata suna Korafi Akan Ba'a Auren yayansu. Alhalin Kuma sun kasa tsayawa su Duba suga Menene ya jefa Su Cikin Wannan Mawuyacin Halin da Suke Ciki.

  Wasu Matan suna cewa Idan Namiji ya Auri Mace a Araha. Matukar Bai ji a Jikinsa ba. Ba zai Rike Wannan Macen da Mahimmanci ba. Wanda Kuma wanann Magana ce da ta Sabawa Mai Lafiyayyen tunani.

  Manzon Allah Saw ya Aurawa Wani Sahabi Mace da ya karantar da ita abinda ya Sani na Alqur'ani. Amma Hakan baisa ya Wulakanta Wannan Matar ba. Sabida an bayar da Auren ne a inda ya dace Kuma ga wanda ya dace. 

  Wanda yake wulakanta mace shine Wanda Bai dace a Bashi Aure ba. Shine Wanda ya San An Aurar Masa Wannan Macen ne sabida abinda yake da Shi na tarin DUKIYA Domin yarinya Tayi Arziki, iyayen yarinya suyi Arziki Kuma idan ya Mutu su ci gadon Dukiyar da ya bari. Wanda idan har Suka Sake Wannan Mijin ya gane Cewar ta Aure shi ne don tayi Arziki a Jikinsa, Haka iyayenta ma sun san zasu Sami Wani Abu daga gare shi ne yasa Suka bashi Auren ta. Zasu fuskanci Wulakanci Kala-kala.

 Tsawwalawa a Zamantakewar Aure ba shine Aure ba. Asalima Yana iya jefa iyayen yarinyar a Cikin Matsalar Cin Bashi. Haka Wanda ya Auri yarinyar ku, Shima zai Fada Cikin bashi, daga baya ya kasa Rike Muku Diyar ku. Domin ana gama biki a daidai Lokacin da ya Kamata ya Sami Nutsua da Matarsa, Yan bashi ne zasu dame shi. Wanda Kuma Hakan ne zai Cire Masa jin dadin Wannan Auren.

  Wallahi Naga Wanda yayi irin Wannan Auren na Tsawwalawa, daga baya gidan da ya sa Wannan Amaryar ma Sai da ya sayar da shi Ya koma gidan haya. Menene Amfanin Irin Wannan. Sai da Auren ma ya Fita daga Kansa. Matar da ya Aura ta Fita daga Kansa, Ya sayar da kayan garar da Akayi Masa. Duk da Haka Bai biya Masa basussukan da Ake binsa ba. Jama'a Menene Amfanin Irin Wannan.?

  Haka zalika zaka ga iyaye suma sun Siyawa Diyar su kayan daki Wanda ya fi karfin Arzikinsu. Daga baya su shiga Cikin takura. Wallahi wannan ma na San Lokacin da Hakan ta faru ga Wani. Ya sayawa diyarsa kayan daki masu Tsada Wanda ya fi Arzikinsa. Wai don ya birge Angon da Yan Uwansa da Mutanen gari masu zuwa Ganin daki. Ya kasa biyan kudin kayan da ya Siyawa diyarsa. Masu Bashi Suka gaji da Alkawarin da Ake yimusu. Daga baya sai dakin yarinyar aka je aka kwashe kayan Aka Basu kayansu. Daga baya abin ya zame wa Wannan yarinyar Abin Gori. Menene Amfanin Irin Wannan?

  Al'amarin Aure kowa yayi daidai karfinsa. Kar ka baiwa talaka Aure Kuma ka zo ka Tsawwala Masa. Idan kunsan zaka Tsawwalawa Wanda ya zo Neman Auren diyar ku. Sai ki bari ku jira Sai Mai Kudi ya zo Tukunna. Shima Kuwa idan Kuka cinye masa jarin kasuwarsa. Kun San Menene zai biyo baya. 

 Duk da Cewar ana iya samu namiji ya je Neman Aure gidan su yarinyar da zai Aura, Yana yimusu karya, yana Nuna Musu Shi Mai Kudi ne, daga baya Kuma Sai Aure ya zo ya Rasa yadda zaiyi.

 Sabida Haka kenan. Duk Wanda ya je Neman Aure, Yana fadin gaskiya Kuma Yana Nuna Musu Zahirinsa, Ba Badininsa ba. Sabida Mata Suna da Wuyar Sha'ani. Duk Lokacin da ka sake ka Nuna Musu kana da tarin DUKIYA. To fa duk Ranar da ka Nuna Musu Cewar baka da shi. Matsala zaku samu.

 A Aure fa Babu Abinda aka Sani Sai Sadaki. Duk Wani Abu da zai biyo bayan Sadaki, Kyautatawa ne. Wajibi Ne Musan Wannan.

  Dan Allah iyaye kuna Saukakawa ga duk Wanda yazo Neman Auren diyarku. Wata Rana zai Zama danku. Sannan yayan da ya Haifa zasu Zama yayanku.


Allah shine Masani

Post a Comment

0 Comments
* Please Don't Spam Here. All the Comments are Reviewed by Admin.


 

 


 


buttons=(Accept !) days=(20)

Our website uses cookies to enhance your experience. Learn More
Accept !